Batun cigaba da tsare wasu mutane sama da 400 da hukumomin tsaro a Najeriya ke yi na kara jawo kiraye-kirayen a bi tsarin da dokar kasa ta tanadar wajen hukunta wadanda ake zargi da aikata laifin tallafawa ‘yan ta’adda da ke addabar mutane musamman arewacin kasar.
Masanin sha’anin tsaro dakta Yahuza Ahmed Getso, ya ce cigaba da tsare mutanen da ake zargin ya sabawa doka, duba da yadda aka samu hujojji kan su.
Idan dai za a iya tunawa, daga karshen watan Februairu ne jami’an tsaro a Najeriya suka fara kamen ‘yan kasuwan canji bisa zargin su da tallafawa ayyukan ta’adanci.
Saurare cikakken rahoton a sauti: