Yanzu haka dai a Najeria musamman ma dai masu mu'amala da kudin dala ta kasar Amurka na cigaba da maida martani game da wannan mataki da Babban Bankin Najeriyan ya ce zai fara dauka tun daga yau, inda ya ce za a dinga bada tukuicin Naira hudu akan kowace dala daya ta Amurka da aka aiko da ita daga kasashen ketare.
Matakin, wanda Babban Bankin Najeriya ya ce na wata biyu ne, wato kwanaki sittin, ya zama tamkar gwaji ga kokarin da gwamnatin Najeriyar ke yi na taimaka wa masu turo da kudi daga kasashen waje bin hanyoyin da suka dace maimakon na sakon hannu da hannu.
Sabon tsarin na Babban Bankin Najeriyan zai shafi masu turo da kudade ne ta kamfanonin kasa da kasa da ke hadahadar kudaden kasashen ketare da aka fi sani da IMO.
Irin wadannan kamfanoni dai sun hada da MoneyGram, da kuma Western Union.
Alhaji Aminu Gwadabe shugaban kungiyar masu canji a Najeria, yace
"Abu ne dai wannan tsare tsaren da shi Bankin tsakiya ke yi a karkashin Gwamnan Babban Bankin, Mr Godwin Emefelle, ni a halin gaskiya ina ganin kokarin jajircewar shi da yake yi na game da tabbatar da cewa wadannan kudade ya tabbatar da ya shigo dasu. In ban manta ba cikin wata biyu ya kawo tsare tsaren da ya ce za a tabbatar da wadannan kudaden suna shigowa. Saboda haka ina ganin kokarin shi. Kuma ina mai kira da ya cigaba da duba duk hanyoyi."
Hanyoyin samun kudin mu na daya ka ga sai dai gurbataccen mai ne, sayar da kayayyakin gona da kamanninsu da kuma masu kawo kudi wadanda ake ce ma portfolio inevestors da kuma direct investors. In ka hada sai ka ga wannan kudin da 'yan Najeriya da suke waje suke turowa ma bai kai su ba. Kaga ba abin da za ai wasa ba ne. Kuma ina ganin shi ya sa shi gwamna ya ga cewa ya dace"
A wata sanarwa dai da Babban Bankin Najeriyan ya fitar ya bayyana cewa akalla Dalar Amurka miliyan talatin ne ake aiko da su daga kasashen ketare a kowane mako, wanda 'yan uwa da abokan arzika ke aikowa 'yan uwansu da ke zaune a Najeriya
A cewar Babban Gwamnan Bankin Najeria Godwin Emefelle, matakin ya biyo bayan irinsu ne da wasu kashashen duniya suke dauka musamman kasar Pakistan da Bangladash wadanda ke da dimbin 'yan kasarsu da ke aiki a kasashen ketare kuma suke samun irin wannan tukuici a duk lokacin da suka aike da kudade zuwa gida.