Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ivory Coast Za Ta Yi Zaben Shugaban Kasa Ranar Asabar


Gobe Asabar al'umar kasar Ivory Coast za ta fita rumfunan zabe domin kada kuri'a a zaben Shugaba kasar da za a yi.

Sakamakon zaben zai fayyace ko Shugaba mai ci Alassane Outtara ya sake samun wa’adi na uku ko akasin haka.

A lokacin da yake yakin neman zabensa na karshe a jiya Alhamis, Outtara ya fada wa dubban magoya bayansa cewa, su fita su kada kuri’a kada su bari a hana su yin zabe, ya kuma fada musu cewa su kare rumfunan zabe.

A cikin 'yan makonnin na an samu karuwar damuwa game da yiwuwar aukuwar tashin hankalin zabe, biyo bayan zanga-zanga da wasu hare-hare a kasar.

An bankawa gidan babban dan takarar adawa Paskal Affi Nguessan wuta, kuma an kai hari a wani ofishin jam’iyyarsa ta Ivorian Popular Front.

Sauran 'yan takara biyu, tsohon shugaba Henri Konan Bedie, na jam’iyyar Democratic of the Ivory Coast, da dan takara Koudio Konan Bertin su ne suke kalubalantar Outtara wadanda suka yi kira ga magoya bayansu da su fita su yi zaben.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG