Gbagbo ne tsohon shugaban kasa na farko da za’a tuhuma a kotun dake birnin Hague, kuma za’a tuhume shine akan aikata laifukan cin zarafin bil’adama da ya hada da fyade, da hallaka jama’a a lokacin rikicin da aka kwashe watanni hudu ana yi, wanda yayi sanadiyyar hallaka mutane 3000.
Rikicin ya kare ne a yayin da Faransa, kasar da ta yima Ivory Cost din mulkin mallaka ta tura dakarunta su maido da zaman lafiya su kuma kama Gbagbo wanda ya buya a gidan gwamnatin kasar a lokacin rikicin.
A jiya laraba ne mai gabatar da karar Fatou Bensouda ya bayyana wa manema labarai cewa Manufar shari’ar itace domin a bankado gaskiya ta hanyar shari’a.
Shima tsohon shugaban matasan kasar Charles Ble Goude zai fuskanci shari’a tare da Gbagbo.
Ambada sammaci domin a kamo uwargidan tsohon shugaban domin yi mata shari’a akan laifukan cin zarafin bil’adama.
A shekarar da gabata ne wata kotun kasar ta yanke mata hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso.