An dai shirya yin taron na ranar Alhamis ne bisa bukatar yin hakan da Amurka tayi tare da goyon bayan wakilai 17 da wasu kasashe ‘yan kallo 25 a cikin hukumar. Ghana itace kasar Afirka tilo da ta goyi bayan ‘daukar wannan matakin.
Wannan shine taron musamman na farko da za’a gabatar tun watan Afrilu, da jami’an hukumar kula da kare hakkin bil Adama suka hadu don tattaunawa kan hare hare da keta yancin ‘dan Adam da kungiyar Boko Haram ke yi a Arewacin Nijeriya.
Taron na ranar Alhamis zai yi nazarin wani vdaftarin kudurin dake neman kwamishinan kare hakkin bil Adama na MDD, Zeid Ra’ad al-Hussein, ya aika da kwararru zuwa Burundi cikin kwanaki 45 domin su gudanar da bincike kan tashe tashen hankulan dake faruwa da neman hanyoyin da za’a kawo karshen su.
Tun cikin watan Afrilu ne dai Burundi take fuskantar tashe tashen hankula bayan da shugaba Pierre Nkurunziza, ya ayyana zai yi tazarce.