Jami’ai a kasar Spain sun ceto kimanin bakin haure 550 da suke bulaguro mai hadari a kan tekun meditareniya yayin da suke kokarin tsallakawa daga arewacin nahiyar Afrika a cikin kwale-kwale.
Jami’an sun ce bakin haure sun cika jiragen kwale-kwale 17, kuma uku a ciki sun niste cikin tekun sakamakon yanayi mara kyau.Hukumomin na Spain sun ce galibin wadanda suka ceton sun fito ne daga arewacin Afrika da kudancin saharar Afrika.
Spain tana kan gaba wajen zama matattarar bakin haure masu kokarin shiga nahiyar Turai domin kaucewa yaki, da ta’addanci da kuma talauci da suke fama da shi a kasashensu.Sai dai har iyau Italiya ce tafi kaurin suna wurin ga bakin hauren saboda tsibiran Italiya sun fi kusa da gabar tekun arewacin Afrika.
Facebook Forum