Kasar Poland ta bukaci jami’an Amurka da su kafa rundunar sojoji tare da zuba dubban dakarun Amurka, a wani mataki na tsorartar da Rasha.
A jiya Litinin, Ministan tsaron kasar, Marius Blaszczak, ya ce a kwanakin nan ya tattauna da hukumomin Washington kan yadda za a kafa matsugunin sojin Amurka na dindindin a kasar ta Poland.
“Wannan kasancewa ta dakarun Amurka a kasar, na da matukar muhimmanci wajen jefa tsoro a zukatan abokanan hamayya, Inji Minista Blaszczak yayin wata hira da ya yi da kafar Radio 1.
Kasar Poland ta jima tana nuna damuwa kan harkokin tsaro a yankin, tun bayan da Rasha ta mallake yankin Crimea daga Ukraine a shekara 2014.
A can birnin Moscow, Kakakin shugaban Rashan, Vladimir Putin, Dmitry Peskov, ya ce, tura karin dakarun yammaci a kusa da kan iyakokin Rasha, “ba zai kara komai ta fuskar tsaro da zaman lafiya a nahiyar ba.”
Facebook Forum