Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sojin Amurka Ya Kashe Kansa A Ofishin Jakadancin Isra’ila A Washington DC


Yan Sandan Rundunar Dogarawan Shugaban Amurka a Kofar Ofishin Jakadancin Isra'ila.
Yan Sandan Rundunar Dogarawan Shugaban Amurka a Kofar Ofishin Jakadancin Isra'ila.

Wani Sojin Saman Amurka ya mutu bayan da ya cinnawa kansa wuta a wajen ofishin jakadancin Isra'ila da ke Washington, D.C., yayin da ya bayyana cewa “ba zai kara kasancewa ba cikin masu kisan kare dangi.”

Sojan Saman mai shekaru 25, Aaron Bushnell, na San Antonio, Texas, ya mutu sakamakon raunukan da ya samu, in ji hukumar ‘yan sandan birni

Bushnell ya yi tattaki zuwa ofishin jakadancin Isra’ila jim kadan kafin karfe daya na rana a ranar Lahadi, kuma ya fara watsa hoton bidiyonsa kai tsaye a kan dandalin yada bidiyo na Twitch, wani wanda ya san lamarin ya shaida wa kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.

Jami’an tsaro sun yi imanin mutumin ya fara daukar hoton bidiyon kansa kai tsaye, inda ya ajiye wayarsa sannan cikin hanzari ya kunnawa kansa wuta.

A wani lokaci, ya ce “ba zai sake kasancewa cikin masu goyon bayan kisan kare dangi ba," in ji mutumin. Daga baya an cire hotan bidiyon daga dandalin, amma jami'an tsaro sun samu sun sake duba hotan bidiyon.

Ba a ba mutumin izinin yin magana a bainar jama'a ba game da binciken da ake yi kuma ya yi magana da AP bisa sharadin sakaya sunansa.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin ta ce, mutumin da ke da hannu a lamarin ya rasu ne a daren ranar Lahadi. Rundunar sojin saman ta ce za ta bayar da karin bayani ba, kwana guda bayan jami’an suka kammala sanar da iyalansa.

Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke neman amincewar majalisar ministocin kasar, domin kai farmakin soji a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, yayin da ake tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi. Harin da sojojin Isra'ila suka kai a Gaza, ya fuskanci suka, ciki har da ikirarin kisan kare dangi a kan Falasdinawa.

Isra'ila ta yi kakkausar suka wajen musanta zargin kisan kare dangi da ake yi mata, ta kuma ce tana gudanar da ayyuka kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada a yakin Isra'ila da Hamas.

A cikin watan Disamba, wani mutum ya kona kansa a wajen karamin ofishin jakadancin Isra'ila a Atlanta, kuma ya yi amfani da man fetur a matsayin makamashi, a cewar hukumomin kashe gobara na Atlanta.

An gano tutar Falasdinawa a wurin da lamarin ya faru, kuma an yi imanin cewa wannan mataki na daya daga cikin “mummunar zanga-zangar siyasa.”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG