Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kasashen Dake Makwabtaka Da Tabkin Chadi


Nigeria Boko Haram
Nigeria Boko Haram

An gudanar taron kasashen dake makwabtaka da Tafkin Chadi domin neman mafita daga matsalar tsaro da ta addabi yankin sakamakon hare-haren Boko Haram.

Muryar Amurka ta zanta da Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu, inda Muhmudu Lalo ya tambeyeshi yadda yake ganin wannan taro da akayi. Ya kuma bayyana cewa abinda yake gani tunda gwamanti ita ke jagorantar komai na al’amarin al’umma, kasancewar ba’a dauki abin da gaske ba a baya to amma canji da aka samu wanda ana tsammanin zai yi tasiri, saboda shugabancin yanzu yana tare da al’umma kuma yana yaki da su masu tayar da kayar baya.

A baya Kyaftin Abdullahi ya fadi cewar irin wannan taron da akayi bazai yi wani tasiri ba, ya kuma bayar da dalilinsa cewa idan da anyi niyyar yakar su to Najeriya kadai zata iya, batare da ta nemi hadin kan kasashen makwabta ba, a dalilin ra’ayin gwamnati wancan lokaci shine makasudin rashin nasara.

Kasancewar makaman da masu tayar da kayar baya ke samu na zuwa ne ta kasashen makwabta Kamaru da Chadi, hadin kan wadannan kasashen zai taimaka wajen dakile makamai da taimako da kungiyar Boko Haram ke samu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:52 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG