Wani gidan da aka adana akwatunan kuri’un da aka jefa a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar Iraqi da aka yi, ya kama da wuta a jiya Lahadi, lamarin da ya sa jama’a suka fara kiran da a sake yin zaben.
Ma’aikatan kashe gobara sun garzaya zuwa wurin, inda suka yi nasarar kashe gobarar a daya daga cikin gine-gine hudu da ke dauke da akwatunan kuri’un da kuma kayayyakin zabe.
Jami’ia sun ce, zai yi wuya a ce gobarar ta shafi akwatunan, sannan suka ce, gobarar ba za ta shafi umurnin da majalisar dokoki ta bayar na a sake kidaya kuri’un ba.
Ya zuwa yanzu, ba a bayyana musabbabin wannan gobara ba, amma Kakakin majalisar dokokin kasar ta Iraqi mai barin-gado Salim Al Jabouri, ya ce da gangan aka saka wutar.
Facebook Forum