Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Bude Wuta a Kasuwar Nahrawan Dake Iraq


Nahrawan Iraq
Nahrawan Iraq

‘Yan sanda a Iraq sunce wani harin kunar bakin wake da aka kai a wata kasuwa mai farin jini dake bayan garin Bagadaza babban birnin kasar, ya kashe a kalla mutane goma sha daya.

Jami’ai sunce a kalla wadansu mutane ishirin da shida suka ji raunuka a harin, da aka kai a kasuwar Nahrawan dake kudu maso gabashin Bagadaza.

Wani jami’in tsaro yace wadansu ‘yan kunar bakin wake guda biyu ne suka bude wuta kan farin kaya a kasuwar jiya Litinin da dare kafin suka tarwatsa kansu.

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin a wani sako ta buga a kafar watsa labaran ta Amaq.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG