Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Akalla Mutane Biyar a Birnin Kirkuk dake Kasar Iraqi


Wurin da aka kai harin kunar bakin wake a Kirkuk, Iraq, jiya, Nov. 5, 2017.
Wurin da aka kai harin kunar bakin wake a Kirkuk, Iraq, jiya, Nov. 5, 2017.

A can kasar Iraq kuma, akalla mutane biyar ne aka kashe a birnin Kirkuk da ake takaddama akai, ta hanyar tashintagwayen bama-bamai a jiya Lahadi.

Sama da mutane goma sha biyu ne suka raunata sanadiyar hare-haren, wanda suka faru minti goma sha biyar tsakanin juna, akan titin Atlas wani wajen hada-hadar kasuwanci a birnin dake da mutane sama da Miliyan.

Wannan hari dai shine irinsa na farko tun da Iraq ta kwace ikon birnin daga mayakan Kurdawa, biyo bayan kada kuri’ar neman ‘yancin cin gashin kai dake zaman bijirewa kasar Iraq da Kurdawa suka yi.

A watan da ya gabata, dakarun Iraqi suka karbe ikon wasu yankuna daga mayakan Kurdawa, ciki har da madatsar ruwan Mosul, bayan kai wani harin sake kwato birnin da kuma wasu rijiyoyin Mai a Arewacin kasar.

Kurdawa dai sun karbe ikon yankin a shekarar 2014, lokacin da mayakan kungiyar ISIS suka yi tashen mamaye yankuna a Arewaci da yammacin Iraqi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG