Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Cafke Wani Ba'amurke


Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Javad Zarif
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Javad Zarif

Hukumomin kasar Iran sun cakfe wani mutum wanda dan kasashe biyu ne, wato Iran din da Amurka a lokacin da ya je kai ziyara ga danginsa dake birnin Tehran.

Makwonni biyu da suka gabata ne Siamak Namazi ya kai ziyara kasar ta Iran wanda ya kasance shugaban wani kampanin hakar man fetur ne dake Dubai

A cewar jaridar Wall Street Journal, rundunar sojan nan ta musamman ta Iran da ake kira “Revolutionary Guardne suka kame shi.

Wannan rundunar dai tana karkashin shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamenini ne, ba gwamnatin Iran ba.

Cafke Namazi na faruwa ne kwannaki kalilan bayanda yarjejeniyar nan da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran kan batun makamashinta na nukiliya, ta soma aiki daga ranar 18 ga watan nan na Oktoba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG