Musayar wutar ta yau Litini ta faru ne a birnin Diyarbakir mai rinjayen Kurdawa, inda 'yan sanda su ka kai samame a gidaje da dama.
Jami'an tsaro sun ce 'yan sanda hudu sun samu raunuka sannan an kama 'yan bindigar uku.
Hukumomin Turkiyya na dora laifin tagwayen hare-haren kunar bakin wake a Ankara babban birnin kasar a farkon wannan makon, wanda ya hallaka mutane 100 kan 'yan ISIS.
Wajen rabin 'yan gudun hijirar Siriya su miliyan hudu, wadanda su ka yi rajista da Majalisar Dinkin Duniya bayan tserewarsa daga Siriya, su na fakewa ne a Turkiyyar.
Yawan 'yan Siriya da ke Turkiyya ya ribanyu fiya da sau biyu tun baya war haka, wanda ya kara nawaya ga makwabtanta.
Jiya Lahadi Shugaban Siriya Bashar al-Assad ya jaddada aniyarsa ta dakile barazanar 'yan ta'adda a Siriya, ya ce hakan zai kai ga mafita a siyasance, wadda mutanen kasar ke bukata don kawo karshen wannan tashin hankali da aka soma tun a watan Maris na 2011.