Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Zata Karbi Naira Miliyan 48 Domin Yin Bincike


Wata ma'aikaciyar kanfanin magunguna tana duban magani
Wata ma'aikaciyar kanfanin magunguna tana duban magani

A shekaru uku masu zuwa, kamfanin hada magunguna na AstraZeneca, zai sa jarin Naira miliyan 48 a binciken magunguna a Nijeriya domin ya gina yawan magunguna da kuma taimakon masana yin bincike.

A shekaru uku masu zuwa, kamfanin hada magunguna na AstraZeneca, zai sa jarin Naira miliyan 48 a binciken magunguna a Nijeriya domin ya gina yawan magunguna da kuma taimakon masana yin bincike.

A lokacin kaddamar da wannan tallafin, shugaban kamfanin na kasar Afirika ta Kudu da kuma Afirika dake kudancin Hamada, Karl Friberg yace niyar kamfanin shine ya dauki nauyin biya ayyuka biyar zuwa bakwai kowacce shekara.

Wannan binciken zai ci kudi Naira miliyan 16 kowacce shekara. Kudaden tallafin bincike na ‘Astra Zeneca Nigeria wani shiri ne domin taimakon bincike da ya shafi cututtukan da ake kamawa daga wadansu da kuma wadanda ba’a kamawa daga jikin wani wata kasa dake Afirika ta Yamma, ya kuma biyo bayan wanda aka kaddamar kwanannan a Kenya a farkon wannan shekarar.

“Rahotanni da suka shafi yawan kamuwa/yaduwa, yadda shan magani ya ke shafar tattalin arziki da yadda kiwon lafiya yake tafiya suna da mahimmanci idan muna so mu fahimci nauyin cututtuka a Afrika. Wannan kudin zai bada damar yin bincike domin samun wadannan bayanan rahotannin.” inji Friberg.

Mayas da hankalin da aka yi akan cututtukan da ake kamawa kamar su kanjamau da zazzabin ciwon sauro a Afrika, yanzu an fadada shi domin ya iya kunsar cututtukan da ba’a samu daga wajen wani kamar su kansa, ciwon suga, ciwon zuciya kamar su hawan jini da asma. “Mun sani irin wadannan cututtukan suna karuwa sosai a kasashen Afrika, amma bamu iya kimanta yawan matsalar da suke kawo ba. Muna bukatar bayanai na kasashe kamin mu san abinda muke yaki da shi - domin mu iya hada hannu da gwamnatoci domin yaki da wadannan matsaloli kuma mu kare yaduwar su da rage kudaden da za’a kashe a wajen yaki da manyan cututtuka,” inji shi.

Friberg yace kungiyarsa ta sani cewa gwamnatin Nijeriya ta damu da karuwar cututtukan da ba’a kamuwa daga wajen wadansu, wannan shi ya sa kungiyarsa suka fito da wannan tallafin.

“Minitan lafiya yana da marmarin kafa shirye shiryen da suka shafi shanyewar jiki, sai dai ya dagara ne ga asibitoci su bullo da kyawawan rahotanni game da manya manayan abubuwan da suke kawo hatsarin ciwon zuciya. Bayan da wannan tallafin, AstraZeneca daukar nauyin wani shiri wanda za’a gudanar a birnin tarayya, Abuja domin a sasance da abubuwan dake kawo hatsarin.

Inji Friberg, “Binciken ya kunshi mutane 5,000 kuma ana yin shi ne tare hadin gwiwa da asibitin kasa dake a Abuja. Wannan ya kunshi Karin kudi dala 100, 000 da kuma an riga ma an fara shi. Muna da fahariya mu ga cewa tun ma kafin a aiwatar da wannan tallafin, mun rigaya mun shiga kokarin taimakawa kiwon lafiyar ‘yan Nijeriya. Ta wurin taimakon wannan shirin, AstraZeneca ya sa kansa a matsayin mai taimako, wajen bincike na wuri da kuma samun magungunan cututtukan zuciya. Wannan zai taimakawa dukan wadanda abin ya shafa – asibitoci, marasa lafiya/al’umma da kuma Astra Zeneca.”

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG