Shawarar da Ministar Kudin Najeriya ta bayar ta sa wa nakasassun Najeriya haraji ta janyo muhawara a matakai daban-daban. Yayin da nakasassun ke cewa sun wahala sun taimaka ma jam’iyyar APC ta ci zabe kuma gas hi ta na nemar ta butulce masu, wasu kuma na ganin sa haraji ma nakasassu zai halatta bara kuma zai ba nakasassun damar yin barar a duk inda su ka ga dama, al’marin da zai haddasa matsala a duk lokacin da ake son kawar da mabarata saboda duk wani dalili. Bugu da kari, a cewar wasu, muddun aka fara karbar haraji daga wajen mabarata, to duk wani kokarin haramta bara zai ci tura.
Sakataren Yada Labaran Kungiyar Makafin Arewacin Najeriya Malam Muntari Saleh, ya ce a ganinsu ma faduwa ce ta zo daidai da zama saboda dama su na wasu korafe-lorafe ganin cewa da sun dauka jam’iyya mai ci za ta kai su tudun mun tsira amma kash.
Malam Muntari ya ce ba a taba ganin nakasassu sun goyi bayan wata jam’iyya ba kamar yadda su ka goyi bayan APC. Ya ce ganin yadda su ka kasa samun biyan bukata duk da irin goyon bayan da su ka baiwa jam’iyyar APC, to idan aka zo zabe nag aba za su shawarci kowa ya yi ta kansa. Ya ce wannan matakin da Ministar kudin Najeriya Mrs Kemi Adeosun ta yi barazanar daukawa zai haifar da sake shawarar siyasa daga bangaren nakasassun.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken hirarsa da Sakataren Kungiyar Makafin Arewacin Najeriya:
Facebook Forum