Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa INEC Ta Dakatar Da Zabe A Wasu Yankunan Jihar Kogi


Wata rumfar zabe a jihar Kogin Najeriya (Hoto: Facebook/INEC)
Wata rumfar zabe a jihar Kogin Najeriya (Hoto: Facebook/INEC)

“Hukumar na mai tabbatarwa da al’umar jihar Kogi cewa, za a kare kuri’unsu kuma za a mutunta abin da suka zaba.”

Hukumar zabe mai zamanta ta INEC a Najeriya ta ce ta dakatar da zabe a wasu sassan jihar Kogi ne saboda rahotanni da suka nuna an yi magudin zabe, musamman yadda aka cike takardun sakamakon zabe tun kafin a kammala zaben.

Cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar, Mohammed Kudu Haruna, INEC ta ce yankunan da wannan al’amari ya shafa da sun hada da kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Manongo, Okehi da Okene.

“Hukumar ba za ta lamunci wannan ba. Duk wani sakamako da ya fito a wadannan rumfunan zaben, ba za a amince da shi ba.” Haruna ya ce.

A cewar hukumar, zaben da aka yi a mazabu tara a kananan hukumomin Ogori/Magongo (Eni, Okibo, Okesi, Ileteju, Aiyeromi, Ugugu, Obinoyin, Obatgben da Oturu) duk an dakatar da su.

“Hukumar na mai tabbatarwa da al’umar jihar Kogi cewa, za a kare kuri’unsu kuma za a mutunta abin da suka zaba.” Sanarwar ta ce.

A ranar Asabar aka gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa a Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG