Simon Lalong wanda tshohon gwamna ne a jihar Filato, ya yi takarar kujerar majalisar dattawa a zaben gama gari na wannan shekara ta 2023 a karkashin inuwar jam'iyyar APC, inda hukumar zabe mai zaman kan ta INEC, ta ayyana abokin takararsa Napoleon Bali na jami'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
A watan Nuwamban da ya gabata ne kotun daukaka kara a Abuja, ta soke zaben Napoleon Bali ta kuma bai wa Simon Lalong, saboda a cewar kotun, jami'iyyar PDP a jihar Filato ba ta da zababbun shugabannin jami’iyya a lokacin da aka gudanar da zaban.
Mai baiwa Simon Lalong shawara kan harkokin yada labarai, Makut Simon Macham, ya ce tuni tsohon ministan ya mika takardar murabus ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Daya daga cikin mutanen kudancin jihar Filato, inda Sanata Simon Lalong ke wakilta, Dindam Longbap Wuyep, ya ce sun yi murna da shigarsa majalisar dattawa saboda zai kawo gyara a jami'iyyar su ta APC a shiyyar.
Shi kuma Idris Zubairu daga kudancin jihar ta Filato ya ce ba su ji dadin yadda Simon Lalong ya shiga majalisar ba, saboda a shekaru takwas da ya yi yana gwamna a jihar Filato, ba su ci moriyar mulkinsa ba.
Yanzu dai ‘yan kudancin jihar Filato sun zuba ido su ga irin rawar da Sanata Simon Lalong zai taka wajen kare muradunsu da kuma nemo musu ayukan ci gaba daga majalisar dattawan.
Saurari cikikken rahoton Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna