Zabubbukan kammala zabe da suka gudana a wasu jihohin Najeriya yau, sun kasance cikin tsari da lumana a wasu rumfunan zabe yayin da a wasu jama'a ba su koyi darasi ba, domin an samu hatsaniya.
Jihohin Sokoto da Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin da ake gudanar da zabububkan
Duk da kasancewa cikin yanayin azumi tun da sanyin safiya ne jama'a suka fito a rumfunan da aka shata gudanar da zaben domin su sauke nauyin da ke kansu.
Akasarin rumfunan zaben an samu zuwan ma'aikata da kayan aiki cikin lokaci tare da soma zaben cikin lokaci musamman a rumfunan da ke kan tituna.
A mafi yawan rumfuna an samar da isassun jami'an tsaro kuma suna kula da yadda al'amurra ke tafiya.
Su ma masu saka ido ga zabe na cikin gida sun rika zagayawa a rumfuna suna lura da yadda zabubukan ke gudana.
Batun sayen kuri'a a lokacin zabe batu ne da ya katin suna a zabubukan Najeriya kuma har yanzu lamarin bai sauya ba, duk da yake ba a fili ake hada-hadar sayen kuri'a ba.
Amma na lura da ana fita shige da fice ana kebancewa da masu zabe ana rubuta sunayensu a wasu rumfuna.
A dukkanin titunan birnin Sokoto kuwa jami'an tsaro sun saka shinge na hana zirga-zirgar jama'a.
Saurari rahoton Muhammad Nasir: