An kyasta yawan al'ummar Najeriya ya haura miliyan 200 kuma Majalisar Dinkin Duniya na sa ran hakan zai ninka nan da shekarar 2050. Hakan zai sa Najeriya ta zama kasa ta uku da ta fi yawan al'umma a duniya inda za ta wuce Amurka, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters.
Alkaluman kidayar jama'a a Najeriya sun shafi rabon kudaden shigar man fetur da kuma wakilcin siyasa a tsakanin jihohi 36 da kabilu 300 na kasar. An caccaki sakamakon kidayar baya bayan da aka samu takaddama tsakanin manyan kabilu uku na kasar wato, Hausa/Fulani, Yarbawa da Igbo.
Shugaban hukumar kidaya ta kasa Nasir Isah Kwarra, ya shaida wa manema labarai cewa za a gudanar da kidayar daga ranar 29 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu, sama da wata guda bayan da ‘yan Najeriya suka kada kuri’a domin zaben sabon shugaban kasa.
Tun a shekarar 2021 ne Najeriya ta tsara yin kidayar jama’a amma hukumomi suka dage aikin saboda kalubalen tsaro, musamman a arewacin kasar da ake fama da tashe-tashen hankula da kuma satar mutane domin neman kudin fansa.