Bisa ga dukkan alamu karuwar mata masu daukar cikin da ba’a shirya masa ba a Najeriya da kuma illolinsa a fannin kiwon lafiya hade da hadurran da kasar ke fuskanta a halin yanzu, ya sa Hukumar kula da yawan jama'a ta kasar tare da hadin kwiwar hukumar kula da yawan al'umma ta majalisar dinkin duniya UNFPA bayyana damuwarsu tare da fitar da rahoto na shekarar 2022 kan wannan batu.
Mahukunta a kasar dai sun bukaci hadin kan al’umma wajen rage matsalar da ke haifar da yawan mace-macen mata da ke zama babban kalubale da mafi akasari lokuta 'yan mata masu karancin shekaru wadanda jikinsu bai shirya daukar ciki da haihuwa ba ke fadawa cikin wannan matsala.
Taken rahoton na bana dai shi ne ‘’Sa ido wajen ganin illar da ke tattare da daukar ciki ko juna biyun da ba a shirya masa ba’’ kuma Cikin wani binciken da hukumar UNFPA ta gudanar, kashi 30 zuwa 40% na mace-macen mata masu ciki ko juna biyu da ake samu na faruwa ne sakamokon daukar cikin da ba’a shirya masa ba, A cewar Honorabul Nasir Isa Kwarra da ke zama shugaban hukumar kula da yawan jama’a ta Najeriya ya kwatanta wannan yanayin a matsayin mafi muni da mata ke shiga.
Hukumar UNFPA ta bayyana cewa a duk shekara ana samun mata miliyan 121 da ke daukar ciki da ba’a shirya masa ba a duniya, kuma daga ciki Najeriya na da kimanin mata Miliyan 2.5, an kuma danganta auren wuri da auren dole har ma da fyade da ake yi wa mata da kuma rashin ilimi da talauci daga cikin abubuwan da ke taka rawa wajen haifar da wannan matsalar kamar yadda Kori Muhammad Habib wakiliyar hukumar UNFPA ta bayyana.
Ministan harkokin mata a Kasar Dame Pauline Tallen ta ce sai da hadin kai za’a shawo kan matsalar, idan aka yi la’akari da muhimmacin rawar da mata da yan’mata ke takawa ga haddin kai da cigaban Najeriya,
Mata da 'yan mata a Najeriya su ke wakiltar kusan rabin al'ummar kasar da adadinsu ya zarce miliyan 210 kuma sama da mata Miliyan daya ne a kasar ne suka ta taba fuskantar wannan matsala ta daukar cikin da ba’a shirya masa ba.
Hakan kuma na faruwa ne a sakamakon garkuwa da 'yan mata da kuma yi musu fyade, har ma a cikin auratayya ana samun hakan.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim: