WASHINGTON D.C. —
Mutane biyu sun mutu yau Alhamis a lokacin da wani makami mai linzame ya fashe a wani sansanin soja a arewacin kasar Rasha.
Ma’aikatar Tsaro ta Rasha, ta ce fashewar ta faru ne a lokacin wani gwajin wata na’ura mai amfani da mai a wani sansanin soji da aka yi amfani da shi don gwajin makamai masu linzame a yankin Arkhangelsk da ke arewa maso yammacin kasar.
Wasu sojoji da injiniyoyi fararen hula su shidda sun sami raunuka, kuma biyu daga cikinsu sun mutu daga baya.
Ma'aikatar tsaron ta ce fashewar ba ta haifar da gurbatacciyar iskar radiation ba.
Wannan fashewar ita ce ta biyu da ta faru a sansanonin soja a Rasha cikin mako guda.
Facebook Forum