Hukumomin kasar Afghanistan sun ce wata mota makare da bama-bamai ta fashe a kusa da wani ginin ‘yan sanda a Kabul, babban birnin kasar a yau Laraba, inda ta kashe akalla mutum 14 da ta kuma matukar lalata gine-ginan da suke kusa.
Mataimakin Ministan Tsaron Cikin Gida na Afghanistan, Janar Khoshal Sadat, ya fada a wani taron manema labarai cewa, fashewar ta kuma jikkata mutum 155, cikinsu har da fararen hula 92.
Ba tare da bata lokaci ba, kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wannan harin, tana mai ikrarin cewa, cibiya ce da ‘yan sanda ke daukan jami’ai da ke yammacin babban birnin kasar.
Wannan mummunan harin da ya hallaka mutane na zuwa ne bayan da kungiyar Taliban ta yi wa al’umar kasar ta Afghanistan gargadin kada su shiga zaben shugaban kasa mai zuwa da za’a yi.
Mai magana da yawun Ministan Harkokin Cikin Gida na Afghanistan, Nasrat Rahimi ya ce, dan kunar bakin waken ya tayar da motar da aka makareta da boma boman a lokacin da jami’an tsaron suka tsayar da shi a wani wurin duba ababan hawa a wajen ofishin ‘yan sandan.
Facebook Forum