China ta yi gargadi mai tsauri ga masu neman canji wadanda suka janyo harkoki a Hong Kong suka tsaya cik, bayan sama da watanni biyu da suka yi suna gudanar da zanga-zanga mai zafi.
Yang Guang, kakakin Hukumar kula da harkokin Hong Kong da Macao, ya fadawa manema labarai yayin wani taron tattaunawa a Beijing a yau Talata cewa "lokaci dan kalila ya rage" kafin shugabannin masu zanga-zangar su fuskanci hukunci."
Makonni da dama da aka yi ana gudanar da wannan zanga-zangar kan tituna, sun jefa cibiyar hadahadar kudade ta Asiya cikin mummunan rikicin siyasa, wanda ba’a ga irinsa ba tun lokacin da Birtaniya ta mika mulki ga kasar Sin a shekarar 1997.
Zanga-zangar dai an fara ta ne a watan Yuni bayan da mazauna garin suka fusata da kudirin dokar mika mutane masu aikata laifuka ga China don su fuskanci hukunci.
A sanadin wannan tashin hankalin aka dakatar da dokar, amma zanga-zangar ta ci gaba kuma tuni ta juye zuwa kira ga neman a canja fasalin mulki na yankin.
Facebook Forum