Da ma can gwamnonin jihohi su kan yi dari-darin aiwatar da hukuncin kisa kan firzinonin da aka yi masu hukuncin kisa. Wasu sukan yi shekara da shekaru suna jiran abun da zai faru da su bayan amincewar kotun koli da hukuncin da aka yi masu.
To sai dai wannan matakin da Jihar Edo ta dauka bai yi wa wasu kungiyoyi da ma mutane dadi ba. Yayin da shugaban kasa ya ba da umurnin wasu sun yi tur da shi suna cewa bai kamata ba.Ko a wannan karon Kungiyar Fafitikar Kare Hakin Bil'Adama ta yi allawadai da abun da gwamnatin Edo ta yi.
Don jin ra'ayin mutane abokiyar aiki Halima ta samu ta zanta da wasu masu sharhi kan harkokin yau da kullum da suka shafi hakin jama'a. Barrister Mohammed Bello Tukur ya ce akwai dokokin da suka ba gwamnatocin Najeriya ikon aiwatar da hukuncin kisa idan kotun koli ta babbatar da hakan. Da Halima ta ce kungiyar Ammnesty International ta yi watsi da aiwatar da hukuncin, sai ya ce hukuncin kisa ana aiwatar da shi ne domin ya zama kashedi ga duk wanda yake son ya aikata laifin da zai kai ga hukuncin . Amma Awal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar dake yaki da zalunci da kare hakin dan Adam cewa ya yi Jihar Edo ta keta doka. Ba daidai ba ne a taye mutane. Ya lashi alwashin kare mutumin dake jiran a rataye shi.
Ga karin bayani a wannan rahoron.