Ofishin jami’an ‘yan sanda na jihar Kogi ya kori jami’an sa uku da aka yi zargin su da hannu wajen fattaucin tabar wiwi.
Kakakin ofishin jami’an ‘yan sanda ASP William Aya, ya tabbatar da haka yau laraba a birnin Lokaja, ya ce an mika ‘yan sandan ga hannun hukumar yaki da sha da fattaucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, domin a yanke musu hukunci.
A cewar sa an kori jami’an ne bayan an same su da hannu wajan aikata laifin a wani gwaji da aka yi musu a dakin amsa tambayoyi na ofishin hukumar.
Jami’in ya kara da cew an bi matakan da suka dace kafin a salleme su daga aiki.
Idan aka tuna, rananr 7 ga watan Nuwamba da ya gabata, kamar yadda mujallar Daily Post wallafa, jami’an humar NDLEA sun damke wani jami’in dan sandan dake rakiya a wata mota da buhuna talatin na tabar wiwi dab da garin na Lokoja.
Facebook Forum