NIAMEY, NIGER - Lura da tashin farashin cimaka da na ababen masarufin da duniya ke fuskanta a halin yanzu ya sa hukumomin Nijar daukan wannan mataki a kasar da illolin canjin yanayi ke tauye ayyukan noman damuna a ‘yan shekarun nan.
A takardar da ya aika wa mambobin Gwamnati da sauran ofisoshin jagorancin lamuran kasa Ministan kasuwanci Alkache Alhada ya sanar da wadanan jami’ai daukan matakin hana fita da hatsi da shinkafa daga kasar da nufin bai wa jama’a damar samun cimakar saye a kasuwanni a daidai lokacin da aka fara fuskantar karancinta a kasashe da dama.
Matakin da shugaban kungiyar ADDC WADATA mai kare hakkin masaya Malan Maman Nouri ke ganin ya yi daidai.
Hatsi da shinkafa na kan gaba a mahimman kayan abincin da ake noma wa a wannan kasa sai dai yawan abinda ake samar wa bai kai adadin bukatun jama’a ba abinda ya sa babban kaso ke shigo wa kasar daga waje lamarin da ya sa Alhaji Habou Ali na kungiyar ‘yan kasuwa ke cewa matakin gwamnatin zai tayar da ‘yan Nijar daga barci.
Wannan na wakana makwanni kadan bayan da hukumomi suka janye harajin taki da na irin zamani da magugunan kwari da dai sauran kayan aikin manoma. Hana fitar da abinci daga kasar zai bada damar tantance tasirin sassaucin da aka yi wa manoma inji shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou.
Kusan ton miliyan shida na abinci ne ake samar wa a kowace shekara a Nijar, sai dai wannan adadi bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da bukatun jama’ar kasar mai yawan mutane million 26 da ‘yan kai saboda haka ya zama dole ‘yan kasuwar kasar ke shigo da kayan abinci daga waje wadanda aka kyasta cewa sun kai gomman miliyoyin ton.
Matsalolin tsaro da illolin canjin yanayi sun yi matukar haddasa koma bayan ayyukan noma a wannan kasa yayinda matsaloli masu nasaba da yaki tsakanin Russia da Ukraine ke haddasa cikas wajen shigo da kayan abinci daga waje.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna