Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Tuhumi Mutane 17 A Kamaru Bisa Zarginsu Da Hannu A Kisan Wani Dan Jarida


Jana'izar Arsene Salomon Mbani Zogo
Jana'izar Arsene Salomon Mbani Zogo

Mutane 17 da suka hada da wani babban dan kasuwa da kuma wani tsohon jami’in leken sirri za su gurfana a gaban kotu a kasar Kamaru akan kisan gillar da aka yi wa wani fitaccen dan jarida, kamar yadda wata takardar kotu da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya gani ta bayyana.

Gawar Arsene Salomon Mbani Zogo, wanda ake kira Martinez, da aka sassare, an gano ta ne kwanaki kadan bayan sace shi a gaban ofishin 'yan sanda da ke wajen babban birnin Yaounde a ranar 17 ga Janairu, 2023.

Dan jaridar mai shekaru 50 da haifuwa yayi suna wajen caccakar zargin cin hanci da rashawa da sanya abokai a mukaman gwamnati ba bisa cancanta ba, a kasar da ke tsakiya Afirka, wanda a lokuta da yawa yake fitowa fili ya fadi sunayen jami'an gwamnati.

Kungiyoyin sa-kai na kasa da kasa sun ce gwamnatin shugaba Paul Biya mai shekaru 91, wanda kuma ya shafe shekaru sama da 41 yana mulkin danniya, tana dakile ‘yan adawa.

Har yanzu dai ba a sanya ranar fara shari'ar wadanda ake zargi ba, da suka hada da Jean-Pierre Amougou Belinga, wani hamshakin dan kasuwa da kuma mai kamfanin yada labaran Anecdote, wanda aka kama makonni biyu bayan kisan Martinez.

Shi ma Maxime Leopold Eko Eko, tsohon shugaban hukumar leken asiri ta Kamaru da ake kira DGRE a takaice, dole ne ya gurfana gaban kotu bisa zarginsa da hannu wajen azabtarwa.

Hakazalika daraktan fannin ayyuka a hukumar DGRE, Justin Danwe, shi ma yana fuskantar tuhuma kan hannu a kisan kai.

Sai dai 'yan kasar Kamaru da yawa na fargabar cewa ba za a yi adalci a shari’ar ba, a kasar da kungiyar 'yan jarida ta Reporters Without Borders ta bayyana a matsayin ta 118 cikin 180 a bangaren 'yancin 'yan jarida.

Bayan da aka saki Belinga da Eko Eko ba tare da wani cikakken bayani ba a watan Disamba, an nada wani sabon alkali, wanda shi ne na uku ya zuwa yanzu, a matsayin wanda zai yi shari'ar.

Kungiyar kare hakkokin bil adama ta Human Rights Watch ta ce ana ci gaba da dakile ‘yancin fadin albarkacin baki a kasar Kamaru, inda ta ce an kashe wasu ‘yan jarida masu zaman kansu 3 a shekarar da ta gabata.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG