Jami’ai a birnin sun gargadi mazauna wurin su zauna a cikin gidajen su ban da wasu yankuna gabar teku guda biyu dake kudancin birnin da guguwar ta addabesu, lamarin da ya tilasta kwashe mutanen wurin.
Masu yawon bude ido sun bar birnin a jiya Juma’a kafin isar guguwar da ake sa ran kadawa yankin da safiyar yau Asabar. Kanfanonin jiragen sama sun dakatar da jigila a yau Asabar.
Cibiyar nazarin harkokin mahaukatan guguwa ta kasa tana sa ran guguwar Barry zata tattaru da karfi kafin ta zuba kuma zata abkawa gabar tekun a matsayin guguwa mai karfi na daya. Zata kuma zama guguwar farko mafi karfi a yankin Atlantic a wannan kaka.
Facebook Forum