Shugaban Amurka Donald Trump ya kira jakadan Burtaniya a Amurka Kim Darroch “sakarai” a wani yunkuri na watsi da rahotan da jakadan ya bayar kan Trump cewa shi “dakiki ne” kuma “maras kwarewa”.
A cewar Trump ta shafin Twitter, “Jakadan Birtaniya wanda ba a maraba da shi a Amurka, ba wani mutum ba ne da aka damu da shi.”
Shugaban na Amurka ya ce Darroch, wanda shi ne babban jami’in diplomasiyyar Birtaniya a Washington tun shekarar 2016, “kamata ya yi yayi magana akan kasarsa da firaminista May, akan tattaunawar ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai, wadda ta kasa idarwa, kuma kar ya ji haushin sukar da na yi kan yadda aka yi shirme wajen gudanar da al’amarin.”
Ya ci gaba da cewa, “na fada wa Theresa May yadda za ta cimma yarjejeniyar, amma ta bi wata hanyarta ta wauta, ta kasa idarwa.
Cikin ‘yan sa’o’i da wadannan kalamai na Trump Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya, Jeremy Hunt ya yi kashedi ga Trump, ya ce masa kalamansa ga Trump da Burtaniya na cike da “rashin mutunci kuma bai dace ba.” Hunt ya ce idan ya zama Firaministan Burtaniya bayan May ta sauka, zai bar Darroch ya cigaba da zama Jakadan Burtaniya a Amurka.
Facebook Forum