A jiya Alhamis ne, Burtaniya tayi zargin cewa, jiragen ruwan Iran, sun yi kokarin toshe hanyar da wani jirgin ruwan dakon man ta zai bi a yankin mashigin Homuz.
A wata sanarwa da gwamnatin Burtaniya ta fitar, ta ce wasu jiragen ruwan Iran guda uku ne suka so su toshe hanyar, amma suka juya da baya, bayan sun samu sakon kashedi na baka daga wani jirgin ruwan yakin Burtaniya.
Sai dai kuma sojojin Iran na musamman, sun musanta zargin da Burtaniya ta yi. Wata sanarwa daga kamfanin dillancin labaran Fars a Iran ta fada cewa, jiragen ruwan sintirin Iran sun gudanar da aikin su ne kamar yadda ya kamata, kuma basu shiga hanyar wasu jiragen ruwa daga wata kasa ba, mussaman ma, jiragen ruwan Burtaniya.
A jiya Alhamis wata mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Morgan Ortagus, ta yi Allah wadai da abunda sojojin ruwan kasar Iran sukai wa jiragen ruwan Burtaniya, ta na mai cewa wannan keta hakkin ‘yancin kasa da kasa ne.
Facebook Forum