Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Fara Daukar Matakan Kare Ambaliya


Biyo bayan gargadi da hukumar bada agajin gaggawa NEMA ta bayar ga al’ummomin dake zaune a gefen kogin Benue a bisa ambaliyar ruwa daga tafkin Lagbo dake kasar Cameroun Hukumomi sun fara daukar matakan kare rasa rayuka da dukiyoyi.

A cewan jamiin NEMA mai kula da shiyar arewa ta tsakiya Abdulsalam Muhammam tuni suka fara fadakar da jamaa da su kaucewa bakin kogin na Benue.

‘’Mashin da aka nuna ya nuna jihohi 11 musammam jihohinda suke daga bakin gabar kogin Benue da Niger abin da ya kama daga Sokoto zuwa su Taraba zuwa Benue zuwa Kogi da kuma Anambra duk jihohin nan da suke bakin gaban ruwa, aka sari sune dai abin zai shafa kuma duk kauyuka da suke bakin gabar tekun nan duk muna ta musu fadakarwa kada su kuskura suyi noma ko su tada wani gini ko suyi shuka ko wani abu na yau da kullun a gaban ruwan nan sabo da idan aka sako ruwan nan daga kogin Lagbo daga Cameroon, duka wadanda suke da gidaje suke da gidaje a gaban wannan kogin idan da hali su nemi wuri inda yan uwan su suke ko dangi ko abokai su bar wannan wuri su koma cikin gari har zuwa karshen shekarar nan, na daya Kenan sannan na biyu masunta kada su bari su sake sai ruwa ya kawo sosa-sosai sannan suce zasu yi su, gaskiya karfin ruwan zai iya tafiya da mutum ALLAH ya kiyaye.

Na ukku manoma idan basu riga sunyi nom aba a gaban ruwan nan to karma su fara, suma masu zuba shara a magudanan ruwa su daina’’.

Ga Zainab Babaji Da cikakken Rahoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG