Ofishin Ministan cikin gida ya yi kira ga al’ummar Nijar da su kwantar da hankalinsu, domin tuni aka ci karfin matasan da ke wannan tarzoma tare da yunkurin tayar da zaune tsaye.
A taron manema labarai da ya kira a ofishinsa da yammacin ranar Alhamis, Ministan cikin gida Alkache Alhada, ya sanar cewa tarzomar matasan da aka fuskanta a kwanakin nan wadda ake dangantawa da zaben da ya gabata, yunkuri ne na masu neman mayar da hannun agogo baya a tafiyar dimokradiyar Nijar, wanda kuma ya ce gwamnati ba za ta laminta da haka ba.
A ci gaba da binciken tushen tarzomar da aka yi fama da ita jami’an tsaro sun kama daruruwan mutane yayin da aka kaddamar da farautar wasu manyan ‘yan siyasa a cewarsa.
A wata sanarwar da ta fitar, kungiyar Mojen mai fafutukatar bunkasa harkokin matasa ta bakin shugabanta Siraji Issa, ta shawarci Alkali mai kare muradun hukuma ya dauki matakin gurfanar da masu hannu a ta’asar da aka tafka daga yammacin Talatar da ta gabata har zuwa ranar Alhamis.
Hukumomi sun tabbatar da mutuwar farar hula daya da jami’in tsaro daya a sakamakon wannan tarzoma da ta haddasa dakatar da harkoki a manyan titunan birnin Yamai, musamman a kewayen kasuwanni da tashoshin shiga mota yayin da abin ya zama tamkar wata hanyar ramuwar gayya akan wasu fitattun mutane.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Mumuni Barma.