Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Zimbabwe: Duk Kuri'ar Da Za a Jefa Za Ta Yi Tasiri


Shugaba Emmerson Mnangagwa yayin da yake magana da manema labarai a Harare, Zimbabwe, July 20, 2018.
Shugaba Emmerson Mnangagwa yayin da yake magana da manema labarai a Harare, Zimbabwe, July 20, 2018.

hukumar zabe a Zimbabwe, tace duk kuri'ar  da aka jefa a babban zaben kasar  da  za'a yi ranar 30 ga watan Yuli idan Allah ya kaimu zai yi tasiri, kuma zata kare sirrin kuri’un da aka kada

Litinin, hukumar zabe a Zimbabwe, tace duk kuri'ar da aka jefa a babban zaben kasar da za'a yi ranar 30 ga watan nan zai yi tasiri, kuma za'a kare sirrin kuri’a. Zabubbukan da aka yi a baya a kasar duk an yi zargin an tafka magudi domin taimakawa jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar.

A rahoton da Sebastian Mhofu ya aiko ma Muryar Amurka daga Harare yace, Mukaddashin shugaban hukumar zaben kasar Emmanuel Magade, yayi magana da manema labarai, da jakadu, da 'yan sa ido a jiya Litinin, da zummar karfafa guiwa kan zaben da za'a yi.


Yace "Tabbacin da zan baiwa jama'a da suka taru anan shine babu wata kumbiya kumbiya wajen tabbatar da kowa zai jefa kuri'arsa cikin sirri. Ra'ayina na kashin kai ne shine babu gudu babu jada baya kan cewa za'a yi kuri'a cikin sirri. Wannan itace tabbacin da nake baiwa hukumomin kasa da kasa,shine kuma tabbacin da nake baiwa al'umar kasar Zimbabwe."

Wannan tabbacin yana zuwa ne a dai dai lokacin da babbar jam'iyyar hamayya MDC tace zata fara zanga zanga daga Talata, idan hukumar ta gaza biyan bukatun da suka gabatar mata da suka hada da tabbatar da cewa ba'a yi magudi a zaben ba.


Jam'iyyar tana zargin hukumar zaben da laifin shirin yin magudi a madadin jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar, kamar yadda tayi zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG