Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Budewa Wasu Direbobin Tasi Wuta a Afrika ta Kudu


Motar safa da aka yiwa ruwan harsashi
Motar safa da aka yiwa ruwan harsashi

Direbobin tasi guda 11 sun mutu, wasu su su 4 kuma sun sami munanan raunuka a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka budewa motarsu wuta a Afrika ta kudu.

Birgadiyan rundunar ‘yan sandan kasar, Jay Naicker ya ce wadanda harin ya shafa suna kan hanyar su ne ta zuwa birnin Johannesburg daga jana’izar wani abokin aikinsu a lokacin da aka kai masu harin, tsakanin garin Colenso da Weenen a lardin KwaZulu-Natal.

Mutane biyu cikin 17 dake cin motar babu abinda ya same su.

Yanzu haka ‘Yan sanda na binciken musabbabin wannan harin, amma kishi tsakanin kungiyoyin direbobin tasi gameda hanyoyin yankin ya taba haddasa tashin hankali a baya.

Kafafen yada labaran Afrika ta kudu sun bada rahoton kisan mutane 10 sakamakon rikicin da ya shafi kishi tsakanin direbobin tasi kirar karamar bas a Cape Town a wani karshen mako cikin watan Mayu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG