Amurka tana nuna damuwa akan alkiblar shirin samun zaman lafiya a Sudan ta kudu, tana mai fadin cewa shugaban kasar Salva Kir, da shugaban yan tawaye Riek Machar, basu nuna halin shugabanci da ake bukata na samun zaman lafiya a kasar ba.
A saboda haka sakatariyar yada labarun fadar shugaban Amurka Sarah Sanders, tace Amurka tana tababar wadannan shugabanni za su yi aiki da zai kai ga kafa mulkin democradiya sahihi, da gudanar da harkokin gwamnati yadda ya kamata a kasar.
A shekara ta dubu biyu da goma sha daya, Sudan ta kudu ta samu yanci daga kasar Sudan, to amma a karshen shekara ta dubu biyu da goma sha uku tarzoma ta barke a kasar akan fafitukar neman iko tsakanin shugaba Kir da tsohon mataimakin sa Mr Machar. Sa’anan kuma an sha keta ka’idar yarjejeniyoyin tsagaita bude wuta.
Bangarorin da suka yi wani taro a birnin Khartoum a makon jiya sun kasa cimma daidaituwa akan daunin iko a tsakaninsu.
Facebook Forum