Da yake jawabi a wurin wani taron manema labarai ministan ayyukan jin kai Alhaji Lawan Magaji ya bayyana irin matakan da gwamnati ke dauka na tallafawa mutanen da wannan bala’i ya afkawa musamman a jihohi hudu da ambaliyar ruwa ta yiwa barna.
Ambaliyar tayi barna a jihohi hudu da suka hada da jihar Agadez inda gidaje tamanin da uku suka rushe, da jihar Maradi inda aka yi hasarar gidaje talatin da takwas. Sai Kuma jihar Tilleberi inda gidaje dari hudu da arba’in da daya suka zube da kuma jihar Damagaram inda aka yi hasara gidaje ashirin.
Gidaje kimanin dari uku ne suka rushe a babban birnin kasar Niamey wanda hakan ya shafi magidanta dari hudu da saba’in da bakwai. Ga baki daya hukumomin sun ce mutane goma sha hudu ne suka rasa rayukansu a wannan ambaliyar da ta addabi kasar.
Ma’aikatar hasashen yanayi na kasar ta ce ambaliyar bana zata shafi mutane dubu dari da hamsin da bakwai. A cewar hasashen yankunan Niamey da Tilliberi da Doso da kuma Tawa ne zasu fi ganin wannan ambaliyar, sai dai gwamnati tace zata fadada matakan nata ne a duk fadin kasar baki daya.
Facebook Forum