Ma’aikatar Agajin Jinkai ta ce fiye da mutum miliyan 2.5 ambaliyar ta shafa a fadin Najeriya.
Baya ga asarar rayuka da dukiya mai yawan gaske, ambaliyar ta yanke wasu sassa da ya zama ba a iya bi a duk lokacin da a ke yin ruwa, kuma zuwa yanzu irin wadannan titunan da lamarin ya shafa suna biyuwa ne don aikin gayya na wucin gadi da jama’a su ka yi.
Sheikh Aliyu Muahmmad Sa’id Gamawa shugaban al’umma ne a jihar Bauchi da ke cewa garin Gamawa na da babbar kasuwa da ambaliyar ruwa ta yanke daga garin da hanyoyin da a ke shiga inda gyarar wucin gadi ne ya taimaka a ke samun kutsawa amma har yanzu akwai inda sam ba ya biyuwa.
Sheikh Gamawa ya aza alhakin kan shugabannin siyasa saboda sakaci ta yadda in a ka yi shiru ma har wata damunar ta zagayo ba za a ga wani matakin da ya dace ba.
A lokacin da ta ke bayani kan illar ambaliyar ruwan, Ministar Harkokin Jinkai, Sadiya Umar Farouq, ta ce gwamnati na daukar matakan hana aukuwar ambaliyar da kuma kare rayukan al’umma.
Sadiya ta ce gwamnati na sane da yawan gonaki ma da ambaliyar ta shafa kuma an raba wa jama’a kayan tallafi.
Da ya ke magana kan ambaliyar Barista Mainasara Kogo Umar ya ce mutane na da hurumin gurfanar da hukumomin gwamnati gaban kotu matukar ba su agaza mu su a lamuran ambaliya ba.
Ambaliyar damunar ta ma raba jihohin kudu da arewa inda hakan ya haddasa karin tsadar farashin fetur da wasu kayan masarufi.
Saurari rahoton: