Hukumar hana shan kwayoyi da mu’amula da su ta kasa NDLEA reshen jihar Ondo, ta kama mutane maza da mata guda 130, a Tsakani watan Janairu zuwa watan Disamabar wannan shekara ta 2016, Alhaji Muhammed Malami Sokoto shine shugaban hukumar a jihar Ondo, ya bayyana cewa sun adadin mutane 130 cikin shekarar nan wadanda suka hada da maza 125, da kuma mata 5, a jihar ta Ondo.
Da yake hira da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, Hassan Ummaru Tambuwal, shugaban ya bayyana cewa sun kama dukkan wadannan jama’ar ne da tabar wiwi da yawanta ya kai kimanin Kilgiram dubu dar hudu da talatin da shida da dari shida da hamsin da shida (kg436, 656).
Shugaban ya kara da cewa jami’an sun sami gonaki wadanda suka kona tabar Wiwi a ciki da yawan tabar ya kai dubu dari hudu da ashirin da tara 429000, wato tone 429 kenan a tsakanin wasu garuruwa dake cikin jihar Ondo.
Alhaji Muhammed Malami, ya kara da cewa jami’an hukumar NDLEA ta kuma kama hodar iblis ko kuma KOKYAN a takaice wadda yawanta ya kai Giram dari biyar, 500g, da shike jama’ar yankin sun fi mu’amula da tabar Wiwi fiye da sauran kwayoyi.
Yanzu haka a cewar sa mutane 43, cikin wadanda hukumar ta kama sun fuskanci shari’a yayinda wasu kuma na tsare suna jiran sharia.
Jama’ar wannan yanki sun raja’a wajan noman tabar wiwi ne sakamakon amfani da gadun daji na gwamnatin jihar Ondo, kuma mafi yawa ba’a amfani da irin wadannan filaye da gwamnati ta kebe a cikin dokar jeji, duk da shike akwai masu gadi, amma bincike ya nuna cewar yawancin masu noma tabar wiwi a wadannan wurare wasu ‘yan kabilar Kwale ne daga jihar Delta.
Ga cikakken rahoton Hassan Ummaru Tambuwal.