Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Bukaci China Ta Yi Karin Bayani Kan Yaduwar COVID-19 A Kasarta


Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), jiya Laraba ta ce tana kira ga kasar China, da ta yi karin bayani kan yaduwar da cutar COVID-19 ke yi a kasarta. 

WASHINGTON, D. C. - “Har yanzu hukumar WHO na mai imanin cewa adadin mace macen da ake bayarwa daga China, ya yi matukar kasa da adadi na hakika, wannan ya shafi irin yadda ake fassara al’amuran, kuma akwai bukatar a karfafa gwiwa ma likitoci da jami’an gabatar da bayanai a bangaren kiwon lafiya na gwamnati su bayyana yaduwar cutar, a maimakon a kashe masu gwiwa,” abin da Michael Ryan, daraktan sashin matakin gaggawa na WHO ya gaya ma manema labarai kenan.


Ryan ya yaba da kokarin China wajen samar da karin gadaje a dakunan jinyar masu tsananin ciwo, da kuma amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta tun a matakin farko na jinya.

Rashin bayanai sosai daga China, ya sa wasu kasashe da dama sun shiga bukatar gwaji ga matafiya daga China.

XS
SM
MD
LG