Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Bi Sahun Wasu Kasashe Da Ke Daukar Matakai Kan Baki Daga China Sakamakon COVID-19


Barkewar cutar COVID-19 a Wuhan
Barkewar cutar COVID-19 a Wuhan

Gwamnatin kasar Ghana ta shiga cikin jerin kasashen da suka dauki matakai kan matafiya daga China a kokarinta na dakile yaduwar cutar COVID-19 da rahotanni suka ce tana yaduwa a China tamkar gobarar daji.

A wata sanarwa da fadar Minstan harkokin wajen Ghana ta fitar, ta ce daga ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2023 hukumomin Ghana zasu bukaci gwajin COVID-19 daga matafiya daga China da zarar sun sauka tashar jiragen saman birnin Accra, ba tare da sun biya kudin gwaji ba.

Hakazalika, ana bukatar matafiyan su nuna takardar shaidar gwaji ta PCR da ke nuna basa dauke da cutar cikin sa’o’i 48 kafin su taso daga China.

Sanarwar ta kuma bukaci al’ummar kasar Ghana su takaita tafiya zuwa China sai dai idan da wani babban dalili.

Matakin gwamnatin na zuwa ne bayan da wasu kasashe suka sanar da daukar tsauraran matakai kan matafiya daga China sakamakon ci gaba da yaduwar cutar COVID-19 da ake gani a China.

Kwararru a fannin kiwon lafiya na Ghana sun jinjina wa gwamnati akan matakin sun kuma bukaci gwamnati ta maida hankali akan iyakokin kasar da ma wasu ‘yan kasar da suka ki karbar riga kafin cutar kamar yadda Dr. Ibuna Faisal, babban jami’a a fannin kula da sashen cututtuka masu yaduwa na kasar ya bayyana.

Sai dai masana a fannin tattalin arziki irinsu Shu’aibu Abubakar, na ganin matakin zai shafi harkokin kasuwanci, ko da yake lafiyar al’umma ta fi muhimmanci a cewarsa.

Ko a baya bayan nan sai da hukumar lafiya ta Ghana ta yi gargadin cewa rashin karbar allurar riga kafin cutar COVID-19 na barazana sosai ga sashen kiwon lafiyar kasar.

Saurari cikakken rahoton Hamza Adam:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00
XS
SM
MD
LG