Ko a shekara ta 2004 mutane Miliyan 3.4 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da wannan cuta adadin da kuma hukumar ta lafiya tace zai iya nunkawa kafin nan da shekara ta 2030.
Abin fargaba dai shine kamar yadda kungiyar masu dauke da wannan cuta ta duniya ta fitar, shine yadda kananan yara yan kasa da shekaru 15 da yawansu ya kai dubu 70 ke kamuwa da nau’in farko na wannan cuta ta sukari a duk shekara.
Shin ko menene mafita game da wannan cuta? Tambayar kenan da wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin, ya yiwa likita Salihu Ibrahim, likitan hada magunguna a Najeriya. Dakta Salihu yace, yanzu ana amfani da magungunan ne domin a samu sauki don kar cutar ta kai ga matsayin da zata lahantar da masu wannan cuta.
A cewar Mallam Hamisu Foni, wani mai dauke da cutar sukari a Najeriya, yace a kalla ya kai shekaru 18 yana fama da wannan cuta, inda yayi ta fama da lalurori masu yawa dalilin cutar sukari.
Sai dai kuma bisa la’akari da wannan cuta ke ci gaba da karuwa a tsakanin mutane manya da kanana, Dakta Salihu yace, ita wannan nau’in cutar ana iya gadarta daga iyaye ko kakanni, amma kuma ba a daukarsa kamar yadda ake daukar wasu cututtuka da suka shafi bil Adama.
Domin karin bayani.