Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Adamawa jam'iyyun adawa sun garzaya kotu akan 'yancin kananan hukumomi


Jihar Adamawa
Jihar Adamawa

Jam’iyun adawa uku sun kai gwamnatin jihar Adamawa kotu bisa kasa gudanar da zaben kananan hukumomi domin maye gurbin majalisun da ta rusa fiye da shekara daya da ya gabata.

Gamayyar jam’iyun sun hada Peoples Party Of Nigeria, Alliance For Democracy da kuma Alliance Congress Party sun bukaci kotu ta haramta shugabacin shugabannin ma’aikata, hana su karbar kaso da gwamnatin tarayya ke baiwa kananan hukumomi da sarrafa su.

Wani lauya mai fashi baki kan harkokin mulkin kananan hukumomi Barr. Sunda Wugira y ace nada kwamitocin rikon kwarya ya sabawa tsarin mulkin kasa, yan mai cewa da kamata yayi a gudanar da zabe kamin sauke tsoffin shugabannin.

Wakilinmu Sanusi Adamu ya yi hira da wasu daga cikin ‘yan adawan da suka hada da Mr, Sunday Amos dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyar PPN a zaben day a gabata da Mal. Njobdi na ACPN inda suka ce ba za su kyale gwamnti ta yi wa dokar kasa karar tsaye ba.

Ga sauran rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG