Babban sakatare na ma'aikatar ayyuka ta jihar Gombe Injiniya Abubakar Bappa Mahmud shi ya tabbatar da aukuwar lamarin wa wakilin Muryar Amurka.
Kodayake dakin ya kone kurmus amma babu wanda ya rasa ransa ko ya jikata sanadiyar gobarar. Inda gobarar ta tashi dakin da manyan mutane suke zama ciki ne yayinda suke jiran shiga jirgi ko kuma karbar manyan mutane.
Wutar ta tashi jim kadan bayan da gwamnan jihar Ibrahim Hassan Dankwabo ya bar filin jirgin saman daga tafiyar da ya yi. Gwamnan ma bai san cewa dakin ya kama wuta ba bayan da ya bar wurin sai da aka sahaida masa.
Kafin a gyara dakin za'a dinga anfani da bangaren masu tafiya kasa da kasa. Haka Injiniya Mahmud yace lamarin ba zai shafi tashi da saukan jirage ba.
Ga karin bayani.