Wakilin gwamnatin Najeriya, Sylvester Evenezer, yayi magana a wajen taron gabatar da rahotan nazarin da hukumar yancin dan Adam ta neman afuwa ta duniya wato Amnesty International ta gabatar mai bukatar kasashen duniya, su soke hukuncin kisa.
Sylvester, yace ai dama Najeriya ta dade karkashin mulkin soja da kayi za ayi maka, shiyasa irin wadannan matakan masu hukunci mai tsanani ba zasu zama abin mamaki ba. Amma tunda Najeriya ta fada mulkin farar hula, wannan mataki na rungumar sassauci ka iya samin nasara, Sylvester ya ci gaba da cewa an gano hukuncin kisa bai dakatar da laifukan da ake yankewa hukuncin ba.
Shima Ambasada Kawo Ibrahim, wanda yake daraktan Amnesty a Najeriya, yace sunyi nazari a kasashen duniya kuma an rage ko kuma tsayar da zartar da hukuncin kisa, an kuma gano laifi ya ragu sosai.
Yawancin mutane sukan amince da aikata laifi ne indan yan sanda suka kama su bayan gana musu azaba.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.