Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta Hana Wasu Manyan Motoci bi ta Kasar


Wasu manyan motoci.
Wasu manyan motoci.

Direbobin sun koka da shugabancin Abdullahi Dikko Inde

Watanni hudu kenan da hukumar kwastam ta kasar Najeriya ta kama wasu manyan motoci shake da kayan da za su kai kasashen Chadi da Kamaru da Ghana wadanda suka dauko daga kasar jamahuriyar Benin. Hukumar ta hana su bi ta Najeriya kuma har yanzu wadannan motoci na tsaye da lodin su ba tare da an gaya mu su dalili ba kamar yadda daya daga cikin direbobin mai suna Abubakar Kiari yayi bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Ba wannan ne karon farko da hukumar kwastam ke tare irin wadannan manyan motocin jigilar kayayyaki ba, kuma direbobin sun ce ko a wancan karo sun nemi bayani amma ba wanda ya ce da su ko uffan.

Wani direban daya daga cikin irin wadannan manyan motoci, Umar Faruk, ya ce kafin zuwan Abdullahi Dikko Inde ba a yi mu su irin wannan tsangwama, ya ce ba su taba shan irin wannan bakar wahala ba sai da Dikko ya hau kujerar shugabancin Hukumar Kwastam din.

Ya ce daga lokacin da sabon shugaban hukumar kwastam din ya kama aiki ya zuwa yanzu sau biyar kenan ana yi mu su irin wannan kamu a hana su ratsawa ta cikin Najeriya.

Motocin dai na kwaso kaya ne daga kasar jamahuriyar Benin su na kaiwa kasashen Chadi da Kamaru da Ghana, kuma galibi kayan matsarufi ne da kuma kayayyakin amfanin yau da kullum.

Wakilin Sashen Hausa a birnin Lagos Ladan Ibrahim Ayawa ne ya hada rahoton kuma ya tattauna da direbobi, kuma ya ce yayi kokarin tattaunawa da kakakin hukumar kwastam din da ke kan iyakar Najeriya da jamahuriyar Benin amma duk kokarin na shi ya ci tura.

XS
SM
MD
LG