Kansancewar bada sanawar ganin watan Azumin watan Ramadan a makare Sheikh Hussain Zakariyah Limamin masalacin Uthman bin Anfan a Abuja yayi Karin haske kamar haka.
Yace” inda mutun ya kwanta ranar shakka,wato ranar da aka ce a fara duba wata na farko,bai san ko za’a ga wata ko ba za’a gani ba, koda yayi niyyar zai yi Azumi, in anga wata ya tashi dashi,yace wannan ba dai-dai bane domin yayi niyya a bisa ga shakka.”
Yakara da cewa “haka kuma sai ya tashi ya ji labari cewa an ga wata to wannan zai kame bakinsa har faduwar rana, amma ba Azumi yayi ba Allah zai bashi lada gwargwadon abinda yayi na biyayya, wanda kuma yayi niyyar idan ana tashi da Azumi zai tashi dashi idan ba’a tashi dashi ba zai ci wannan shima bashi da Azumi kuma babu damar ci ko sha domin abunda yayi wata ibada ce tya masamman wace Allah zai bashi lada akan ta, haka kuma wanda ya tashi bai ji labarin anga wata ba har ya ci wani abinci, da zaran yaji anga wata sai ya bar cin abincin na bakinsa ma ya fito dashi itama wannan wani akin Ibada ne .”
Har ila yau Malamin, yace” idan mutune yace shi tunda bai yi niyya ba zai ci abinci a cikin watan Ramadan to Allah zai yi hushi dashi domin yak eta haddin wannan wata mai alfarma wanda Allah ya haramta ci da sha da jima’i a cikinsa da rana don haka inda zai rayu duk rayuwarsa yana Azumi don ya biya wannan wuni dayan bai isa ya biya ba .