Za’a yi amfani da shudin kati ne domin mayar da dan wasa saniyar ware, kwatankwacin yadda ake hukunta ‘yan wasan kwallon Rugby.
Hakan zai zamo tamkar wani ci gaba ne akan amfani da katin gargadi mai launin rawaya kuma za’a fi amfani da shi ne wajen hukunta ‘yan wasan da suka bijirewa umarnin alkalin wasa.
Jim kadan bayan bayyanar wannan rahoto, aka fara yada jita-jita akan yadda za’a aiwatar da amfani da wannan kati a manyan gasoshi irinsu firimiyar ingila da la-ligar kasar sifaniya. saidai sanarwar da hukumar fifa ta fitar a baya-bayan nan ta fayyace lamarin.
A wani salon sako irin na kafafen sada zumunta, hukumar kwallon kafar duniyar ta bayyana cewar babu kamshin gaskiya a batun bullo da irin wannan kati a manyan gassanin kwallon kafa kuma hakan yayi wuri.
Hukumar ta FIFA ta kara da cewar ba za’a aiwatar da duk wani shiri na bullo da shudin kati ba sai an fara jarraba shi a kananan gasoshi tukunna.
Dandalin Mu Tattauna