Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kungiyar UEMOA Ta Gudanar Da Taro A Birnin Yamai


Taron kungiyar UEMOA a Yamai
Taron kungiyar UEMOA a Yamai

Wasu jami’an gwamnatin Jamhuriyar Nijer da na hukumar kungiyar kasashen Afrika ta yamma rainon Faransa, wato UEMOA, sun fara gudanar da taro a birnin Yamai da nufin tantance ci gaban da kasar ta Nijer ta samu ko akasin haka game da alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar kai da kawon al’umomi da dukiyoyinsu a tsakaninta da sauran kasashe 7 masu amfani da kudaden sefa (CFA).

Waiwaye akan ayyukan da gwamnatin Nijer ta dauki alkawarin gudanarwa a fannonin da ke shafar rayuwar talakawa kai tsaye shine babban makasudun wannan taro dake matsayin wani ma’aunin fayyace kokarin kasar ta Nijer, akan maganar mutunta yarjejeniyar da ta cimma da sauran takwarorinta na yammacin Afrika rainon Faransa, inji Aicha Saidou, jami’a a ma’aikatar Ministan Fasalin kasa.

Fannin sufuri na daga cikin fannonin da talakkawan yankin na UEMOA su ka fi korafi akansu, ganin yadda jami’ai a wasu kasashe mambobin wannan kungiya ke fatali da ‘yancin kai-komon jama’a, sai dai Oumar Moussa da ke daya daga cikin wakilan ma’aikatar sufuri ta kasa na cewa, sakacin matafiya ne ke karawa baragurbin ma’aikata kwarin gwiwar ci gaba da tafka irin wannan ta’asa.

Wannan shi ne karo na 6 da ake gudanar da irin wannan taro na binciken ayyukan da gwamnatin Nijer ta zartar a karkashin kungiyar UEMOA a tsawon shekara, kuma a cewar Djibo Ibrahim na ma’aikatar kudi ta kasa, a shekarar 2017 sun yi ayyukan da aka kiyasta cewa, sun haura kashi 54 daga cikin 100 na alkawuran da suka dauka a bara, an samu ci gaba da kashi 65 kuma a wannan karon inda da kwarin gwiwar za a samu ci gaban da zai sa su tunkari kashi 100 cikin 100.

A karshen wannan taro na tsawon wuni 3, mahalartan zasu bullo da wasu shawarwarin da za su taimaka a magance matsalolin da ke haddasa tsaiko wajen zartar da ayyukan da kungiyar ta UEMOA ke shata wa gwamnatocin kasashen Afrika ta yamma, rainon Faransa su kimain 8.

Ga cikakken rahoton Wakilin muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG