Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Kungiyar Jama'ar Tsakiyar Arewacin Najeriya


Tambarin kungiyar
Tambarin kungiyar

Wata kungiya mai suna North Central People’s Forum ko kuma Kungiyar Jama’ar Arewa Ta Tsakiya an dade da kafa ta sai dai yanzu ne Shugaban amintattun kungiyar, Laftana JanarJeremiah Timbut Useini ya kaddamar da mambobin kwamitin da zai gudanar da Kungiyar.

Shugaban ya ce kungiyar ta samu goyon bayan yawancin tsoffin shugabanin kasar irin su Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da Janar Abdulsalami Abubakar da Janar Yakubu Gowon wadanda dukansu za a ce su 'ya'yan kananan kabilun Arewacin kasar ne wadanda aka fi sani da Middle Belt Forum a turanci.

Abin da ya dauki hankali a kaddamar da komitin gudanarwar shi ne cewa wannan kungiya za ta fi karbuwa ga jama'ar jihohin Arewa 6 da babban birnin tarrayya da suka kunshi kungiyar, ganin cewa Arewa ta tsakiya yanki ne da ke zayyane a kundin tsarin mulkin kasa a matsayin yanki daya cikin yankuna 6 na kasar Najeriya.

Amma ga kwararru a fannin zamantakewa, akwai kalubale sosai a matsayin kungiyar kananan kabilu na Najeriya domin babu shi a kundin tsarin mulki a matsayin yanki na kasar.

Shugabannin da aka kaddamar sun hada da Arc. Gabriel I. Aduku a matsayin shugaban kwamiti, da Alhaji Abdullahi Oji a matsayin mataimakin shugaba, Bolaji Kaleel shi ne babban sakataren kwamiti na kasa, sannan Onorabil Audu Sule shi ne sakataren yada labarai.

Shi kuwa shugaban kananan kabilu na Arewacin Najeriya Mark Amani yana ganin kungiyar na kunshe da wasu manufa na daban, saboda a cewar sa ba kowa da kowa ne ya san da zamanta a tsakanin kananan kabilu ba.

Saboda haka Amani na mai ganin wasu ne ke neman cimma wani buri nasu.

Mark Amani na mai ganin a hada maza da mata da ma matasa a wuri daya domin su san suna da kungiyar da ke bi masu hakokinsu, domin yana ganin har yanzu ana azabtar da mutane tare da bautar da su, kenan a ganin Mark Amani, mutane ba su da 'yancin su har yanzu a tsakanin kananan kabilun kasar baki daya.

Sai dai ga tsohon shugaban kungiyar matasa Kiritoci na Arewa Pasto Simon Dolly ya ce kungiyar ta yi yunkurin hada kan 'yan Arewa ta yadda za su zama tsintsiya madaurin ki daya.

Shi ma shugaban amintattun kungiyar, laftana Janar Jeremiah Timbut Useini mai murabus ya kara jadadda wa shugabanin kwamitin da su dauki kansu a matsayin muryar wakilan jihohinsu da mutanensu.

Janar Useini ya bukace su da su binne bambance-bambancen su na addini ko kabilanci ko na siyasa domin su hada kai don ci gaban jama'arsu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

An Kaddamar Da Kungiyar Jama'ar Tsakiyar Arewacin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00


XS
SM
MD
LG